in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta mayar da hankali wajen rushe gine-ginen da aka yi su kan hanyoyin ruwa domin kaucewa cigaba da fuskantar ambaliyar ruwa a yankuna daban daban
2013-08-14 15:56:23 cri


Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake samu a `yan kwanakin nan a jihar Kano yana haifar da ambaliya a wasu unuguwannin dake cikin birnin Kano.

Har dai yanzu hukumomi a jihar basu kammala tantance yawan asarar da wannan ambaliyar ruwa ta haifar ba.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba a acikin shekaru biyu da jihar Kano ke fuskantar barazana ta ambaliyar ruwa sakamako zubar ruwan damuna kamar da bakin kwarya da ake samu.

Ko a bara an samu makamancin wannan annoba wadda ta haifar da asarar rayuwa da kaddarori masu yawa, lamarin daya janyo hankulan kungiyoyin bayar da agaji na gida da na kasashen ketare wajen tallafawa wadanda wannan matsala ta shafa.

Duk da cewa gwamnatin jihar Kano a wancan lokaci ta dauki matakai domin tabbatar da ganin irin wanann matsala ta mabaliyar ruwa bata sake faruwa ba, amma bisa dukkan alamu har yanzu akwai gagarimin aikin a gaban gwamnatin bisa la`akari da yadda aka samu ambaliyar ruwa a unguwannin daban daban da cikin birnin Kano.

Kafin faduwar damunar ta bana , jihar Kano ta fado cikin jerin jahohi da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Tarayya Najeriya NEMA ta lasafto wadanda akayi hasashen zasu gamu da wannan annoba ta ambaliyar ruwa a damunar bana.

To amma a firar dana yi das hi kwamshinan yada labarai na jihar Kano Farfessa Umar Faruok Jibril ya shaida mun cewa tun kafin sanarwar hukumar ta NEMA gwamnatin jihar kano ta kwana da sanin za a fusknaci wannan matsala, kuma batayi wata-wata ba ta fara daukar matakan kandagarki.

Ya cigaba dacewa shekaru biyu baya gwamnatin jihar Kano ta fara aikin gina sabbin hanyoyin ruwa tare da gyara wadanda ake dasu, haka kuma hukumar lura da kwashe shara ta jihar ta himmatu wajen kwashe tarin sharer da ake zubarwa a cikin magudanan ruwa

To yanzu tun da hakan ta faru wani mataki ya ragewa gwamnati?

Kwamashinan yada labaran na jihar Kano yace abu na farko shin e a dukufa addu`a domin ganin irin wannan annoba bata sake faruwa ba, sannan kuma jama`a su guji zubar da shara a kan hanyoyin ruwa , haka kuma ya tabbatar mun dacewa gwamnati zata kara mayar da hankali wajen rushe duk wani gini da aka yi shi kan hanyoyin ruwa a cikin birnin Kano da kewaye.

Unguwannin da wanann matsalar ta ambaliyar ruwa ta fi shafa sun hadar da Unguwar Zango dake yankin karamar hukumar birnin, da Fagge da Darmanawa da kuma unguwar Kofar Mata.(Garba Abdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China