Jonathan ya fadi haka ne yayin da yake ganawa da wakili na musamman na firaministan kasar Thailand Dr. Surapong Tovichakchaikul a birnin Abuja.
Shugaba Jonathan ya ce yana farin-cikin ganin cewa, ma'aikatun harkokin waje na kasashen biyu sun riga sun gano wasu sabbin fannoni karfafa dangantaka tsakaninsu, tare da nuna fatan cewa Thailand zata zama wata muhimmiyar aminiya ta Najeriya, musamman ma a ayyukan gona da albarkatun ma'adinai.
A nasa bangaren, wakili na musamman na firaministan kasar Thailand, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar kana ministan harkokin waje na Thailand Dr. Surapong Tovichakchaikul ya jinjina irin ci gaban da gwmnatin Goodluck Jonathan ta samu a cikin shekaru biyu da suka gabata, musamman ma a fannin zirga-zirga, inganta samar da wutar lantarki, ilimi da kuma kara fadada fannonin tattalin arziki.
Har wa yau kuma, Mista Surapong ya bayyana kudurin kasar Thailand na karbar bakuncin taro tsakanin Thailand da Afirka a watan Fabrairu na shekara ta 2014, wanda ke da nufin bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin kasar Thailand da kasashen Afirka.(Murtala)