A cikin wata sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Dr. Reuben Abati ya bayar, an ce, shugaba Jonathan ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da Babban dan kasuwar Najeriya Alhaji Aliko Dangote, da sauran wasu manyan masu zuba jari da masu bankuna na kasar a ofishinsa dake fadar gwamnati a Abuja.
Sanarwar ta ce, Jonathan ya tabbatar da ce gwamnatinsa na dukufa ka'in da na'in wajen kawar da duk wani cikas ta fuskar zuba jari a Najeriya inda ya yabawa shirin da kamfanin Dangote ya tsara, wato na kafa matatar mai mafi girma a Afirka da masana'antar samar da takin zamani a Najeriya, haka kuma ya nuna yabo ga kokarin da bankunan kasar suke yi na samar da rancen dala biliyan 3.3 a wajen wadannan ayyuka.
Shugaba Jonathan ya lura cewa jarin da kamfanin Dangote zai zuba a fannonin tace mai da takin zamani da sauransu zai taimaka sosai wajen samar da dimbin guraban ayyukan yi ga al'ummar Najeriya, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar da kyau kuma cikin sauri.(Murtala)