An ce kawo wannan lokaci bangarorin biyu suna ci gaba da dauki ba dadi.
Bisa bayanin da wani jami'in rundunar 'yan sanda ya bayar, an ce, an kai wani dan bindiga guda asibiti, bayan da aka samu nasarar cafke shi, kuma kimanin maharan 10 ne ke ci gaba da jan daga a wani kantin saida kayayyaki dake wannan cibiyar kasuwanci.
Bugu da kari, bisa labaran da aka samu daga kafofin watsa labaran wurin, an ce, yanzu haka akwai mutane da dama da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Shugaban ofishin 'yan sandan birnin Nairobi Benson Kibue ya bayyana cewa, da sanyin safiyar jiya Asabar ne wasu mutane dauke da makamai suka shiga cibiyar kasuwancin dake kira Westgate, sa'annan zuwan 'yan sanda ya haddasa musayar wuta tsakanin bangarorin Biyu.
Bugu da kari wani wanda ya ganewa idonsa aukuwar lamarin ya ce, masu dauke da makamai sun jefa gurneti, inda nan da nan mutane suka tarwatse daga cibiyar kasuwancin. (Maryam)