in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya da Kenya za su rattaba hannu kan jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa
2013-09-05 10:25:24 cri

Kasashen Kenya da Najeriya za su sanya hannu kan jerin yarjejeniyoyin huldar dangantaka a yayin wata ziyarar da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai kai a wannan kasa a ranar Alhamis, a cewar wani babban jami'in gwamnatin kasar Kenya. Sakatariyar harkokin wajen Kenya Amina Mohamed ta shaida wa 'yan jarida a ranar Talata a birnin Nairobi cewa, kasashen biyu na shirin rattaba hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci, haraji, kare zuba jari da sauransu.

Ziyarar shugaban kasar Najeriya ta zo bayan ziyarar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a wannan kasa dake yammacin Afrika a cikin watan Julin wannan shekara. Ziyarar shugaba Jonathan ta kwanaki uku za ta kasance ta farko ta wani shugaban kasar waje tun bayan da sabuwar gwamnatin kasar Kenya ta kama aiki a cikin watan Afrilu.

Madam Amina Mohamed ta bayyana cewa, ziyarar mai zuwa ta shugaban kasar Najeriya za ta kasance mai muhimmanci wajen kafa wani kwamitin hadin gwiwa domin bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu. Haka zalika, wakiliyar gwamnatin Kenya ta jaddada cewa, kasashen biyu na fatan kyautata kasuwanci tsakanin kasashen nahiyar Afrika.

A nasa bangare, jakadan kasar Kenya dake Najeriya mista Tom Omollo ya bayyana cewa, akwai wajabcin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu ta fannin al'adu da ilmi. Haka kuma mista Omollo ya nuna cewa, wannan ziyara za ta kasance ta farko ta shugaban Najeriya a kasar Kenya cikin shekaru 25 da suka gabata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China