Kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samo mana labarin cewa, yanzu haka fadan kabilanci a Kenya ya yi sanadiyar salwantar rayukan mutane fiye da 20, sannan fiye da 15 suka ji rauni a ranar Laraban nan a garin Moyale dake kan iyaka da arewacin kasar.
A safiyar wannan rana, fadan ya barke tsakanin kabilar Borana da Gabra dake Moyale a karkashin gundumar Marsabit, wadda nisanta bai kai kilomita daya ba daga kasar Habasha da suke makwabtaka da juna, abin da ya kawo fargaba ga mazauna wannan yanki.
Asalin rashin jituwa a tsakanin kabilun biyu ya fara ne tun a watan Disamban shekarar 2011 game da maganar rabon arzikin kasa, kamar ruwan sha da burtalin dabbobinsu, duk dai cewar, ana kara alaka da siyasa a ciki.
Gundumar Moyale dake kan iyaka a kasar daga arewacinta da kasar Habasha ya zama fagen daga na tashin hankali tsakanin kabilin biyu na Borana da Gabra. A watan Febrairu ma, fiye da mazauna kasar ta Kenya 30,000 suka tsallaka zuwa makwabciyarta Habasha sakamakon tashin hankalin da ake yawan fuskanta a yankin.
Ofishin MDD mai kula da harkokin jin kai OCHA ya ce, hukumomin kasar Habasha sun tabbatar da cewar, 'yan kasar ta Kenya sun tsere zuwa makwabtansu sakamakon fadan da ake yi wanda ya zama na ramuwar gayya tsakanin kabilun. (Fatimah)