in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kotun laifukan duniya ta sake bude shari'ar mataimakin shugaban Kenya
2013-09-11 11:00:11 cri

Babbar kotun laifukan duniya ICC dake Haque na kasar Holland a ranar Talatan nan 10 ga wata ta sake bude shari'ar mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto wanda ake zargi da laifuffukan cin zarafin dan adam.

Ruto, 'dan shekaru 47, tsohon 'dan majalissar dokokin kasar lokacin da aka yi rikicin zabe a shekara ta 2007 ya zama babban 'dan siyasa na farko da yake fuskantar shari'a dangane da wannan rikicin.

Banda Ruto, shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta da wani 'dan jarida Joshua Arap Sang su ma ana zargin su da magudin zabe na shugaban kasar wanda shi ne ya kawo tashin hankali a shekara ta 2007-2008 da ya salwantar rayukan mutane akalla 1100, sannan fiye da dubu 650 suka rasa muhallinsu.

A ranar 5 ga watan Satumban wannan shekarar ne kasar ta Kenya ta so janye shari'ar daga kotun duniya wadda ta shiga cikin kasashen masu hulda da ita tun shekara ta 2005, sai dai kafin ta iya janyewa daga cikin al'amurran kotun sai ta sanar da magatakardar MDD a rubuce, haka kuma janyewar zai dauki shekara guda.

A karkashin tsarin, wajibi ne kasar ta Kenya ta cigaba da ba da hadin kai ga duk wata shari'a da kotun za ta yanke har zuwa lokacin da wa'adin janyewarta ya cika. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China