Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ta fidda wasu bayanai, dake kunshe da shirin daukar karin matakan tsaro a birnin Mombasa dake gabar ruwa, wanda kuma ya kasance daya daga muhimman garuruwa dake karbar dimbin 'yan yawon shakatawa masu ziyartar kasar.
Da yake karin haske ga manema labaru don gane da wannan batu, kwamandan rundunar 'yan sandan shiyyar Robert Kitur, ya ce, akwai cikakkun bayanai dake nuna cewa, kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaida, na shirin kaddamar da wasu hare-hare cikin mako mai zuwa, wadanda za su dace da lokacin tunawa da ranar rasuwar malamin addinin nan mai suna Sheik Aboud Rogo, wanda aka yiwa kisan gilla.
Wadannan bayanai da tuni aka yada su ga cibiyoyin tsaron kasar, a cewar Kitur, sun ba da damar daukar karin matakan tsaron musamman a wuraren taruwar jama'a.
Birnin Mombasa, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a kasar ta Kenya, a baya bayan nan na shan fama da hare-haren gurneti, da garkuwa da baki 'yan kasashen waje, daga maharan kungiyar Al-Shabaab, lamarin da ya sabbaba yanayin zaman dar dar, ya kuma gurgunta hada-hadar yawon shakatawa da a baya birnin ya shahara da ita. (Saminu)