in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici a tsakanin kabilun kasar Guinea ya haddasa mutuwar mutane kimanin 100
2013-07-26 14:39:45 cri
A ranar 25 ga wata, kakakin gwamnatin kasar Guinea Moussa Dadis Camara ya fada wa wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, kwanan baya, rikicin da ya barke tsakanin kabilu daban daban a birnin N'Zerekore na kasar ya haddasa mutuwar mutane 98, tare da jikkatar wasu sama da 130.

Camara ya ce, yanzu, akasarin mutanen da suka jikkata sun samu sauki, kuma halin da ake ciki a wurin ya samu farfadowa, kuma yanzu, ana gudanar da ayyuka da zaman rayuwar jama'a yadda ya kamata, amma sojoji na ci gaba da kasancewa a birnin N'Zerekore da sauran biranen da ke kusa da shi, don maganin sake barkewar rikicin.

Bisa labarin da aka samu, an ce, yanzu, an riga an cafke mutane sama da 130 da ake zaton suna da hannu a rikicin da ya shafa, kuma sojoji sun kame dimbin makamai da aka samu a wurin, kuma yanzu, hukumomin shari'a na wurin na gudanar da bincike game da batun, Camara ya ce, za a bayar da sakamakon binciken.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China