Wannan muradi mai girma wanda kuma za'a iyar aiwatarwa, in ji mista Sall a yayin bikin kaddamar da tsarin CMU.
A halin yanzu, kashi 20 cikin 100 ne kawai na 'yan Senegal suke cin gajiyar wannan shiri, in ji shugaban kasar Senegal.
Haka kuma a yayin wannan biki, ya mika takardar banki ta kudin Sefa biliyan 1.7 ga wakilan gidauniyoyin kiwon lafiya na yankunan kasar daban daban, kudin da zai shiga wajen aiwatar da shirin CMU.
"Gurina shi ne na bai wa dukkan 'yan kasar Senegal a lokacin da suke bukata na samun kulawa mai kyau ta fuskar kiwon lafiya ba tare da wata matsalar kudi ba da kuma wani hadarin kudi ba. Domin haka ne muka zuba wadannan kudade na sefa biliyan 1.7 domin bukasa gidauniyyar kiwon lafiya, in ji mista Sall. (Maman Ada)