in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Senegal ya jinjinawa hadin gwiwa tsakanin Sin da kasarsa
2013-07-11 11:02:40 cri

Firaministan kasar Senegal, Abdoul Mbaye ya nuna yabo da babban ingancin dake kasancewa kan huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da Senegal, a yayin da yake karbar makullan filayen wasannin uku da aka kammala gyaransu bisa shirin maido da martabobin filayen wasannin jihohin kasar bisa taimakon dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. 'Ina nuna yabo kan muhimmiyar hadin gwiwa dake tsakanin Senegal da Sin. Ina fatan za ta cigaba da zurfafa domin moriyar al'ummomin kasashen biyu.' in ji firaminista Mbaye bayan ya karbi wadannan kiluluwa daga hannun jakadan kasar Sin dake kasar Senegal, mista Xia Huang. Bisa wannan shiri na gyare gyare, mista Abdoul Mbaye ya bude a ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata filin wasa na Caroline Faye dake birnin Mbour mai tazarar kilomita 80 da birnin Dakar da kasar Sin ta gyara a lokaci guda tare da filin wasa na Massene Sene dake birnin Fatick na tsakiyar kasar. Mista Mbaye ya bayyana farin cikinsa kan namijin kokarin da kasar Sin take yi na tallafawa manufar wasannin motsa jiki a kasar Senegal, musammun ma a fannin gine-gine. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China