Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya bar birnin Dakar a ranar yau Laraba zuwa kasar Rasha inda zai halarci taron kungiyar kasashen G20, a cewar hukumomin kasar a ranar Talata.
Mista Sall zai halarci taron G20 da zai gudana daga ranar 5 zuwa 6 ga watan Satumba a birnin Saint Petersburg a matsayinsa na shugaban kwamitin sabuwar dangantakar cigaban Afrika (NEPAD). Haka kuma wannan ita ce ziyarar farko ta shugaban kasar Senegal a kasar Rasha.
Jakadan kasar Senegal dake birnin Moscow, Mamadou Saliou Diouf ya bayyana cewa, akwai yiyuwar wata ganawa tsakanin shugaban kasar Senegal da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin a yayin wannan babban taro na G20.
A cewar mista Diouf, ganawa tsakanin Sall da Putin za ta taimaka wajen karafafa dangantaka tsakanin kasashen biyu, da batun zuba jarin kasar Rasha da za a tattauna tsakanin gungun tuntubar juna kan kasar Senegal a birnin Paris na kasar Faransa a watan Oktoba mai zuwa. Haka kuma a halin yanzu, jarin da kasar Rasha take zubawa a kasar Senegal ya shafi wasu fannonin noma, harkar sanadarin Phosphates da kuma sarrafa kifaye. (Maman Ada)