Tsofuwar ministar shari'a ta kasar Senegal, Aminata Toure, an nada ta faraminista a ranar Lahadi domin maye gurbin mista Abdoul Mbaye, kuma ita ce mace ta biyu a kasar Senegal da ta rike wannan mukami tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai a shekarar 1960. Kafin ita, tsohon shuagabn kasar Senegal, Abdoulaye Wade ya nada ministar shari'arsa madam Mame Madior Boye kan kujerar faraministan kasar a cikin watan Maris na shekarar 2001. Sabuwar faraministan din ta yi sanarwa bayan nadinta cewa, ta karbi wannan kujera cikin murna, tare da jaddada niyyar yin biyayya da aiki tukuru bisa wannan sabon nauyi tare da gaggauta cigaban ayyukan da tsofuwar gwamnati ta yi tun shekarar bara. An haifi madam Toure a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 1962 a birnin Dakar kuma tana daga cikin manyan kusoshin jam'iyyar shugaba Macky Sall. Hakazalika ta yi fice wajen kasancewa ta hannun damar shugaban kasar Senegal, sannan kwararra a fannin ilimin tattalin arziki, harkokin masana'antu da kudi, kuma ta yi aiki a asusun MDD kan al'umma a Afrika da kuma a cibiyarsa dake birnin New York. Haka kuma a tsawon lokacin da ta rike kujerar ministan shari'a, ta taimaka wajen kawo gyare gyare da sabbin manufofi a tsarin shari'a na kasar Senegal, da yaki da cin hanci da kuma karbe dukiyar kasa daga hannun manyan jami'an tsofuwar gwamnatin Albdoulaye Wade. Madam Toure tana da jan aiki a gabanta na tada komadar tattalin arzikin kasar bisa hagen shugaban kasar Senegal a cikin lokacin da jama'ar kasar suke fuskantar tsadar kayayyakin bukatun yau da kullum, da matsalar ambaliyar ruwa da kuma yanayin matsalar kudin kasa da kasa. (Maman Ada)