A wannan rana, kwamandan sansanin sojojin ruwa na Ikot Abasi a jihar Akwa Ibom dake bakin tekun kudancin kasar Issak Ogebole ya fada wa kafar yada labaru cewa, bayan da masu kamun kifaye na wurin suka gaya wa sojojin ruwa inda 'yan fashin teku suka buya, sojojin ruwa sun kai samame tare da kashe 'yan fashe teku 6, da kuma jikkata wani daga cikin 'yan fashin tekun.
A yayin da kasashen duniya suke kokarin yaki da 'yan fashin teku na kasar Somaliya da ke yankin gabashin kasar, al'amura sai kara rincabewa suke yi dare da rana, amma har yanzu 'yan fashin teku na shiyyar tekun Guinea da ke yammacin Afrika na ci gaba da kara aikata abin da ba shi ne ba. A shekarar 2011, hukumar kula da harkokin teku ta kasa da kasa ta mayar da tekun Guinea a matsayin sabon sansanin 'yan fashin teku, tare da yin kashedi ga jiragen ruwa da ke ratsa wannan wuri.
Tuni a wannan wata, sojojin ruwa na Nijeriya sun kashe 'yan fashin teku 12 a tekun ne Guinea.(Bako)