in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC na kasar Sin ya fara ziyara kasar Najeriya
2013-09-18 21:55:35 cri

A ranar Talata 17 ga wata da dare ne, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC Mista Zhang Dejiang ya iso Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, wanda a yau wato ranar Laraba, ya gana da ma'aikatan ofishin jakadancin Sin dake Najeriya, da kuma Sinawa mazauna da kuma aiki a Nigeriya a otel din Transcorp Hillton. Yanzu ga rahoton da wakilinmu Murtala ya aiko mana.

A lokacin ganawar Mista Zhang Dejiang ya ce, wannan ziyarar nashi ya zama karo na farko da shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC ta kasar Sin a wannan zagaye ya kawo a Najeriya, kuma an zabi Afirka don ta zama zango ta farko. Wannan ya shaida cewa, gwamnatin kasar Sin na mayar da hankali sosai kan raya dangantakar abokantaka tsakaninta da Afirka.

Ya ce, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka na bunkasa da kyau kuma cikin sauri a fannoni da dama, ciki har da tattalin arziki, kasuwanci, cinikayya, siyasa, haka kuma al'ummar bangarorin biyu suna kara samun fahimtar juna.

Mista Zhang Dejiang ya ce, Najeriya babbar kasa ce a nahiyar Afirka, wadda ke bunkasa cikin sauri a wadannan shekaru. Sannan kuma akwai kamfanonin kasar Sin da yawa, ko na gwamnati ko masu zaman kansu, wadanda ke zuba jari da gudanar da ayyukansu a nan Najeriya. Saboda himma da kwazon da Sinawa dake aiki a kasar suke yi, kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu wajen inganta hadin-gwiwa da mu'amala tsakanin kasashen biyu.

A karshe dai, Mista Zhang Dejiang ya jinjinawa kokarin da Sinawa ke yi a nan Najeriya, kuma ya yi fatan za su ci gaba da nuna hazaka ta fuskar karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Najeriya.

Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Transcorp Hillton, Abuja, Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China