Sin na fatan kotun manyan laifukan duniya za ta girmama ra'ayin jama'ar Kenya
A ranar Laraba 18 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, jama'ar kasar Kenya sun zabi Uhuru Kenyatta da William Ruto a matsayin shugabanninsu ta hanyar jefa kuri'a. Ana fatan kasashen duniya za su girmama ra'ayin jama'ar Kenya, da fatan kotun manyan laifukan duniya za ta saurari abin dake zukatan kasashen Afirka da na kungiyar AU.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku