Amurka ta sake nanata cewa za ta dauki matsayin ba ruwanta kan batun tsibirin Diaoyu
A kwanan baya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki ta sake bayyana cewa, Amurka za ta dauki matsayin ba ruwanta kan batun mallakar tsibirin Diaoyu. Game da wannan batu kuma, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin Hong Lei ya bayyana a ranar Laraba 18 ga wata a nan birnin Beijing cewa, ana fatan Amurka za ta cika alkawarinta, ta gudanar da ayyuka cikin taka-tsamtsam, a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da kuma dangantaka tsakanin Sin da Amurka.
Mr. Hong ya jaddada cewa, tun asali daman kasar Sin take da mallakar tsibirin Diaoyu da wasu tsibiran dake kewayensa, a bayyane yake cewa Sin ta nuna matsayinta kan batun tsibirin.(Fatima)