in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinawa da ke kasar Amurka sun aika da wasikar nuna adawa ga gwamatin kasar kan matsalar tsibirin Diaoyu
2013-02-21 16:31:12 cri
Kafin zuwa ranar da firaministan kasar Japan Shinzo Abe zai kai ziyara a kasar Amurka a ranar Jumma'a 22 ga wata, a madadin duk Sinawa da ke Amurka, wakilai daga cikinsu, sun mika wata wasikar nuna adawa ga Shinzo Abe ta hanyar ofishin jakadancin Japan da ke kasar Amurka a ran 20 ga wata, inda suka yi Allah wadai da Japan bisa tsokana da take yi ga mulkin kai na kasar Sin, musamman game da batun tsibirin Diaoyu.

A cikin wasikar, Sinawa da ke Amurka sun bayyana cewa, idan aka yi la'akari da tarihi ko labarin kasar, tsibirin Diaoyu da sauran tsibiran da ke kusa da shi sun kasance yankunan kasar ne ta Sin. Amma a watan Satumbar bara, gwamnatin Japan ta dauki matakai bisa radin kanta don sayen tsibirin, abin da ya lahanta babban tushen amincewa juna tsakanin kasashen Sin da Japan. Yanzu, gwamnatin Japan na yunkurin yin gyare-gyare game da tsarin mulkin kasar, da kara kasafin kudi wajen harkokin soji, da gyaran sunan sojojin tsaron kasar, tare da musunta laifuffukan da suka aikata yayin yakin duniya na biyu, abin da zai kawo babbar matsala ga kasashen da ke yankunan Asiya da Pasific da sauran duniya baki daya, kuma a karshe dai, ita ma Japan za ta fuskanci tarin kalubale don gane da hakan.

Sannan kuma, Sinawan da ke kasar ta Amurka suka aika da tallatacciyar wasika ga shugaban kasar Barack Obama, da sakataren harkokin wajen kasar John Forbes Kerry, da shugaban majalisar dokoki John Boehner yau da kwanaki 2 da suka wuce, inda suka bukaci shugaban Obama da ya sanar da Shinzo Abe wanda ke shirin ziyarar kasar cewa, matakan tsokana da Japan ta dauka ya kawo kalubale ga tsarin dokokin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kuma kasashen duniya ba za su amince da hakan ba, kana kuma, ya zama wajibi a kayyade matakan da masu tsattsauran ra'ayi na Japan suke dauka, don hana sake bullowar masu ra'ayin nuna karfi a Japan, in ba haka ba, hakan na iya kawo wata babbar masifa ga kasashen Asiya da sauran kasashen duniya cikinsu har da kasar ta Amurka.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China