Ranar 3 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba yi, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin mista Hong Lei ya nuna cewa, Sin na mai da hankali sosai tare kuma da matukar nuna rashin jin dadi kan dokar hukumar tsaron kasar Amurka na shekarar 2013 wadda a kawai gyaran fuska da ya shafi batun tsibirin Diaoyu.
An ce, kwanan baya, majalisar dattijai ta kasar Amurka ta zartas da wannan gyararren shirin dokar, wadda ta sanar da cewa, Amurka ba ta dauki matsayi kan ikon mallakar tsibirin Diaoyu ba, amma a sa'i daya ta amince cewa, kasar Japan ce ke da iko a tsibirin. Kuma babu wani mataki da wani bangare zai dauka wanda zai canja matsayin da Amurka ta dauka kan wannan batu.
Hong Lei ya ce, tsibirin Diaoyu da sauran kananan tsibirorin dake kusa da shi dukkansu suna karkashin mallakar yankin kasar Sin tun fil azal, ko kadan babu wata takaddama kan wannan batu. Amurka ta bayyana sau da dama cewa, ba za ta nuna goyon baya ga wani ba game da rikicin yankin kasa tsakanin Sin da Japan, saboda haka Sin nafatan Amurka za ta cika alkawarin da ta dauka bisa la'akari da zaman lafiya da karko a wannan yanki, abin da ya fi kyau shi ne ta taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da karko a wannan yanki. (Amina)