in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kintsawa Japan koda batun tsibiran Diaoyu na iya kazanta
2013-01-16 19:57:11 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei, ya fada a ranar Laraba cewa, Sin tana cikin shirin kota-kwana koda al'amura game da tsibirin Diaoyu na iya kazanta.

Hong Lei ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martini game da rahotanni da kafofin watsa labarai suka bayyana cewa, a ranar Talata ministan tsaron japan Itsunori Onodera, ya bayyana wasu kamalai na daukar wasu matakai kan kananan jiragen sintirin Sin da ke shawagi a saman tsibiri Diaoyu kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.

Bugu da kari ya nanata kin amincewar Sin na shigar jiragen sama da na ruwa na Japan cikin yankunan ruwa da sararin saman tsibiran Diaoyu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China