A ranar Jumma'ar da ta gabata ne dai sakatariyar harkokin wajen Amurkan ta halarci wani taron manema labaru na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen kasar Japan Fumio Kishida, wanda aka gudanar a birnin Washington na Amurka, a inda ta bayyana cewa, Amurka ba ta dauki wata matsaya ta daban ba don gane da wancan tsibiri na Diaoyu, sai dai ta ce, tsibirin na karkashin ikon kasar Japan a hukunce, ta kuma kara da cewa, kasarta ba za ta goyi bayan dukkanin wani yunkuri da ka iya gurgunta ikon Japan din don gane da tsibirin ba.
Wannan dai kalamai na Clinton, a cewar Qin, ya nuna a fili yadda ta gaza fahimtar ainihin hakkokin kasashen dake takaddama kan tsibirin na Diaoyu. Bugu da kari mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ya ce, wajibi ne a fahimci ikon da Sin ke da shi kan wannan tsibiri, da ma ragowar tsibirai wadanda bisa tarihi da dokokin kasa da kasa ke karkashin mallakar kasar ta Sin. Idan kuwa aka kalli musabbabin takaddamar dake wanzuwa don gane da wannan batu, Qin na ganin Japan ce ke da alhakin dukkanin matsalolin da ake fama da su, domin ita ce ta nace bin hanyar da ba ta kamata ba, tare da nuna ikon mallakar yankin, wanda sam ba ya karkashin ikon ta tun asali. Wannan kuwa al'amari ne da a cewarsa ba wani boyayye ba ne ga idon duniya.(Saminu)