Dangane da furucin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan ta yi na cewa, bunkasuwar rundunar kasar Sin na sauya yanayin tsaro a wannan yankin da take ciki, kuma Sin tana kokarin canza odar da ake bi a yanzu, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar 21 ga wata a nan Beijing cewa, har kullum kasar Sin a tsaye take tsayin daka kan adawa da ayyukan da Japan take yi na keta ikon mulkin kasar Sin a tsibirin Diaoyu da tekun da ke kewaye da shi.
Mista Hong ya kara da cewa kasar Sin na da aniya da kuma kwarewar kiyaye ikon mulkin kasa a tsibirin na Diaoyu.(Tasallah)