in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon faraministan kasar Togo zai kama aiki bada jimawa ba
2012-07-22 16:51:55 cri
Sabon faraminstan kasar Togo, Ahoomey-Zunu Artheme Seleagodji da ya fito daga bangaren masu adawa zai kama aiki a ranar Litinin mai zuwa bayan kammala bikin mika iko da misalin karfe goma sha daya na safe agogon wurin tare da faraministan da yayi murabus mista Gilbert Houngbo a wani labari da kamfanin Xinhua ya samu daga wata majiya mai tushe a ranar Asabar.

An nada mista Seleagodji a matsayin sabon faraminista a ranar 19 ga watan Yuli kuma zai maye gurbin Gilbert Houngbo wanda ya mika takardar murabus da kuma ta gwamnatinsa a ranar 11 ga watan Yuli.

Ahoomey-Zunu Artheme Seleagodji ya rike mukamin ministan kasuwanci a cikin tsofuwar gwamnatin tun cikin watan Maris na shekarar 2010 tare da mukamin sakatare janar na fadar shugaban kasa, mukamin da ya rike tun daga watan Janairun shekarar 2008. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China