Kungiyar tarayyar Turai EU za ta cigaba da tallafawa kasar Mali, musammun ma domin cika alkawuran da ta dauka a yayin taron Brussels na watan Mayun da ya gabata, in ji manzon musamman na kungiyar EU game da yankin Sahel, mista Michel Reveyrant De Menthon a ranar Talata a birnin Bamako.
Mista De Menthon ya yi wannan kalami bayan ganawarsa tare da faraministan kasar Mali Oumar Tatam Ly.
Jim kadan bayan wannan ganawa, mista De Menthon ya shaida wa manema labarai cewa, sun tattauna tare da faraministan kasar Mali game da al'amuran baya bayan nan da suka faru a cikin kasar, tare da bayyana jin dadinsa kan cigaban da aka samu kan shirin maido da zaman lafiya. Haka kuma mista De Menthon ya nuna amincewarsa da imaninsa bisa niyyar shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da faraministansa ga neman bakin zaran warware wannan matsala ta hanyar siyasa.
A cewar jami'in EU, kasar Mali ta fahimci cewa, mafitar wannan rikici na dogaro da demokaradiyya da kuma zabe.
Ziyarar mista De Menthon a kasar Mali, ta zo kwanaki biyu kafin wani bikin tunawa da bikin rantsar shugaba Ibrahim Boubacar Keita da zai samu halartar shugabannin kasashen waje da dama. (Maman Ada)