Wakilin musamman na sakatare janar na MDD game da batun kasar Mali, Albert Gerard Bert Koenders wanda ke ziyarar aiki a yanzu haka a birnin Alger na Aljeriya ya bayyana a ranar Litinin cewa, dakarun MDD na cigaba da isa kasar Mali domin taimakawa gwamnatin Mali warware matsalolin da suka biyo bayan rikicin da kasar ta fuskanta tsakanin shekarar 2012 da ta 2013. 'Muna nan muna tura dakarun MDD a kasar Mali domin taimakawa sabbin hukumomin kasar domin waraware matsaloli na bayan rikici.' in ji mista Koenders a gaban manema labarai bayan wata ganawarsa tare da ministan harkokin wajen kasar Aljeriya Mourad Medelci. 'Mun tatttauna kan muhimmancin sabon shirin al'umma da na siyasa tare da yankin arewacin kasar Mali da jiran abubuwa da dama daga shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita tare kuma da jaddada muhimmancin nauyin dake kan wuyan tawagar MINUSMA.'
Haka zalika jami'in ya ce, an samu kyautatuwar yanayin tsaro da zaman lafiya a cikin wannan kasa dake yankin Sahel, haka kuma jami'in na MDD ya nuna cewa, samun zaman lafiya a kasar Mali sai ya biyo ta kyautatuwar zaman lafiya da cigaban yankunan arewacin kasar da suka yi fama da yake-yaken kungiyoyin kishin islama da sojojin kasar Faransa da na Afrika a cikin watannin da suka gabata. (Maman Ada)