in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a maido da kungiyoyi masu makamai kan teburin shawarwari don sasanta 'yan Mali
2013-09-13 10:57:42 cri

Shugaban kungiyar 'yan tawayen Larabawan Azawad (MAA), Mohamed Ould El Oumrany ya bayyana a yayin wani taro a Bamako cewa, duk wata hanyar sasanta 'yan kasa, to ya kamata 'yan kasar Mali su daina duba baya, kana a maido da kungiyoyi masu rike da makamai kan teburin shawarwari, duk da illar da suka janyo wa kasar Mali, ganin cewa yarjejeniyar da aka cimma a Ouagadougou a ranar 18 ga watan Junin da ya gabata, kan amincewa da kare 'yancin kasa da cikakken yankin kasar Mali a matsayin kasa daya tak. Mohamed Ould El Oumrany ya yi wannan furuci a lokacin da yake amsa wata tambaya kan alakar dake tsakanin kungiyarsa ta MAA da kungiyar MNLA. A yayin da yake tabo dangantakar dake tsakaninsu, El Oumrany ya nuna cewa, 'Dangantaka ce ta yankunan kasa. Muna zaman tare cikin yankin guda. Wannan dangantaka tana kara hare-hare, da hadasa barna idan babu jituwa, to irin wannan abun ne ya faru a garin In Khalil inda 'yan tawayen MNLA suka kwace dukiyoyin al'ummar Larabawa dake kasuwanci a wurin. Muna fatan za'a warware wannan matsala da hanyar biyan mutane dukiyoyinsu da su yi asara na biliyoyin kudaden Sefa.' in ji mista El Oumrany. Haka kuma a lokacin da aka tambaye shi ko yana da hurumin magana da sunan kungiyar MAA, mista El Oumrany ya amsa cewa, dukkan kungiyoyin 'yan tawaye suna iyar magana da sunan junansu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China