Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali ya jagoranci zaman farko na majalissar zartaswar kasar, kwana guda bayan kafa sabuwar gwamnati da firaminista Oumar Tatam Ly zai jagoranta.
Yayin zaman majalissar da ya gudana jiya Litinin, shugaba Keita ya ja hankalin mambobin majalissar da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya ce, Mali ta sha fama da tarin matsalolin da suka haifar ma ta da koma baya, don haka sabuwar gwamnatin ta zo daidai lokacin da ake matukar bukatar kafa sabon tarihin ci gaban kasa.
Sabuwar majalissar zartaswar kasar dai na kunshe ne da mambobi 34 da suka hada da mata 4, da kuma ministoci 6 da ke cikin gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta gabata.
Wata majiyar fadar shugaban kasar ta Mali ta shaidawa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua cewa, daukacin ministocin kasar sun samu halartar zaman majalissar na ranar Litinin, ban da daya guda dake kasar waje. (Saminu)