in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama wajibi a tabbatar da yanayi mai kyau a Kidal, in ji shugaban MINUSMA
2013-09-17 11:12:16 cri

Bayan an kai hari kan wata tawagar manyan jami'an gwamnatin kasar Mali a yankin Kidal a ranar Lahadin da ta gabata, wakilin musamman na sakatare janar na MDD a kasar Mali, kuma shugaban tawagar MINUSMA, mista Bert Koenders ya bayyana muhimmancin tabbatar yanayin tsaro mai kyau a yankin Kidal, da kuma kasar Mali baki daya, a cewar wata majiyar MDD a Bamako, babban birnin kasar Mali. A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Litinin, shugaban tawagar MINUSMA, Bert Koender ya yi Allah wadai da hadarin da ya faru a Kidal ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba, inda wasu masu zanga-zanga suka tare tawagar manyan jami'an gwamnatin Mali. Wannan tawaga dake karkashin jagorancin ministan sasanta 'yan kasa da cigaban arewacin Mali, Cheick Oumar Diarrah tare da takwaransa na hukumomin kasa, na tsaro da kuma gwamnan Kidal.

Mista Koenders ya bayyana muhimmacin cimma yanayin tsaro mai kyau a yankin Kidal da ma sauran yankunan kasar baki daya. Haka kuma ya yi kira ga bangaori daban daban da al'ummomin kasar da su yi aiki tare wajen cimma shawarwarin da za su taimaka wajen samun zaman lafiya mai karko bisa tushen kudurin mai lamba 2100 na kwamitin sulhu na MDD da yarjejeniyar Ouagadougou da aka cimma a ranar 18 ga watan Junin da ya gabata, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China