in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar shugaban majalisar NPC ta kasar Sin a kasashen Afrika muhimmin matakin diplomasiyya ne da Sin ta dauka game da Afirka
2013-09-17 16:38:48 cri

Bisa goron gayyatar da shugabar majalisar dokokin kasar Uganda Rebecca Alitwala Kadaga, da shugaban majalisar dattijan Nijeriya David Mark da shugaban majalisar dokokin kasar Aminu Tambuwal suka yi masa, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) Zhang Dejiang ya fara ziyara a kasashen daga jiya 16 ga wata, baya ga kasashen, zai kuma ziyarci Slovak da Rasha bisa goron gayyatar da takwarorinsa na kasashen suka yi masa. Kafin ya fara ziyarar, darektar kwamitin kula da harkokin waje ta majalisar wakilan jama'a ta kasar Sin Madam Fu Ying ta yi bayani kan muhimmancin wannan ziyara.

Wannan ziyara ta kasance wani muhimmin matakin da kasar Sin ta dauka ta fannin diplomasiyya da ya biyo bayan ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai Afrika a watan Maris na wannan shekara, wanda ya nuna yadda sabbin shugabannin kasar Sin suke dora muhimmanci kan huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma karfafa fahimtar juna da hadin gwiwa tsakaninsu.

Madam Fu Ying ta ce, Kasar Sin da kasashen Afrika na da dankon zumunci a tsakaninsu, bayan da kasar Sin ta aiwatar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, kuma kasashen Afrika suke gaggauta bunkasuwarsu, akwai makoma mai haske wajen raya hadin gwiwa a tsakaninsu. Na farko, bangarorin biyu za su kara samun moriyar juna a fannin tattalin arziki, a shekarar 2009, kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya ta farko ga kasashen Afrika, abin da ya sa aka kara bukatar yin ciniki da saka jari a tsakaninsu. Na biyu kuma, an kara yin mu'amala a tsakaninsu, ban da mu'amalar da ke tsakanin gwamnatocin kasashen biyu, an kara cudanya tsakanin jama'arsu. A karkashin tushen raya dangantakar bangarorin biyu daga dukkan fannoni, an kara yin mu'amala da hadin gwiwa a karkashin inuwar bangarorin daban daban. Na uku shi ne, ba a samu wani babban sabani a tsakaninsu ba, kasashen Afrika da Sin sun mayar da bunkasuwar da ko wannensu suka samu tamkar damar samun cigaba ga juna, kuma nasarar da Sin ta samu ta karfafa gwiwar kasashen Afrika, abin da ya taimaka wajen raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, kuma abin da ya sa hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta kara bunkasa cikin gaggawa.

A watan Maris na bana, yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyara a kasashen Afrika, ya bayyana cewa, huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ba za ta tsaya ba, kullum tana ta ci gaba da bunkasa, yadda za a raya huldar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika bisa yanayin da ake ciki, ya zama babban aikin da aka sanya a gabanmu. Don haka, a wannan ziyararsa, Shugaban majalisar NPC ta kasar Sin Zhang Dejiang zai dora muhimmanci kan sabon yanayin da ake ciki da kuma sabbin bukatun da ake fuskanta wajen raya huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika. A hannu daya, zai isar da sako na kara raya dankon zumunci da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da inganta hadin gwiwa a tsakaninsu ga kasashen Afirka. A hannun dayan kuma, zai saurari shawarwari da ra'ayoyin da shugabannin kasashen Afrika ke da shi, don nuna cewa, kasar Sin tana fatan inganta hadin gwiwa da kasashen Afrika wajen kafa dokoki.

Madam Fu Ying ta kara da cewa, sabbin shugabannin kasar Sin sun dauki tsayayyiyar aniya ta yin hadin gwiwa da sada zumunta da kasashen Afrika. Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke ziyara a kasashen Afrika, ya siffanta alakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, tamkar "abin da ya taba hanci, ido sai ya yi ruwa".

A game da yadda wasu kasashen yammaci ke zargin kasar Sin da yin mulkin mallaka na sabon salo a Afirka, Madam Fu Ying ta ce, furucin bai samu karbuwa ba a Afirka. Ta ce, an taba yi wa kasashen Afirka mulkin mallaka, kuma jama'ar Afirka sun san mene ne mulkin mallaka. Yanzu hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika na ba da babbar gudummawa ga kasashen Afrika. Duk da cewa, wasu kasashen yammacin duniya sun mai da hankali sosai game da albarkatun kasa da Sin ta shigo daga nahiyar Afrika, amma a hakika dai kasashen yammaci sun fi shigowa da albarkatun kasa daga Afirka. Alal misali Afirka ta fitar da kashi 2 cikin 3 na man fetur dinta zuwa kasashen Turai da Amurka, kuma kasar Sin da kasashen Afrika suna samun moriyar juna da nasara tare a hadin gwiwar da ke tsakaninsu ta fannin albarkatun kasa.

Har wa yau, a game da fannonin da ya kamata a daidaita a kokarin da ake na kara bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, madam Fu Ying ta ce, ya kamata bangarorin biyu su kara fahimtar juna da biyan bukatun al'ummominsu don inganta hadin gwiwa a tsakaninsu. Kana kuma, ya kamata bangarorin biyu su tashi tsaye don gaggauta yunkurin bunkasa masana'antu a kasashen juna. Na uku, ya zama wajibi a inganta mu'amalar jama'a a tsakaninsu. Na hudu, ya kamata masana'antun kasar Sin da ke kasashen Afrika su kara daukar alhakin da ke wuyansu.

A takaice dai, kasar Sin za ta nace ga bin manufar amincewa da juna a fannin siyasa, da hadin gwiwa da juna da samun moriyar juna ta fuskar tattalin arziki, da yin mu'amala da juna a fannin al'adu, don kara inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da ke tsakaninta da kasashen Afrika.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China