Shugaban a cikin wata hira da ya yi da kafar watsa labarai ta Rasha '24 channel', kuma kamfanin dilancin labarai na kasar Syrian ta ruwaito, ya ce, ko duk wani irin yaki da aka kai kan kasar Syria zai shafi yankin gaba daya kuma zai saka daukacin yankin a cikin tarin matsaloli da rashin kwanciyar hankali na shekaru masu zuwa nan gaba.
A cewar kamfanin dillancin labaran kasar Syria SANA, wannan furuci na shugaba Assad ya zo ne kwanaki bayan da gwamnatinsa ta amince da tayin da kasar Rasha ta yi mata game da mika makamanta masu guba karkashin sa idon kasa da kasa, don kaucewa harin soja da Amurka ke barazanar kai wa kasar bisa zargin kai hari da makamai masu guba a Damascus a watan da ya gabata.
A sakamakon shiga tsakanin Rasha, shugaba Assad ya ce, aiwatar da wannan niyya ta gwamnatinsa, ya danganta ne ga bangaren Amurka idan ta amince ta jingine duk wani kiyayya da take nuna ma kasarsa. (Fatimah)