in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ya gana da manzon musamman na kungiyar AU kan batun Somaliya
2011-11-01 16:32:58 cri
A ran 31 ga wata, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, Ablet Abdrexit ya gana da tsohon shugaban Ghana, kana manzon musamman na kungiyar AU kan batun Somaliya, Jerry John Rawlings da 'yan rakiyarsa a nan birnin Beijing.

Ablet Abdrexit ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kokarin da MDD da kungiyar AU da kasashen Afirka suke yi wajen daidaita batun Somaliya, tare da taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga yunkurin tabbatar da zaman lafiya a Somaliya tare da sauran kasashen duniya baki daya. Sin tana dora muhimmanci sosai kan dangantaka tsakaninta da Ghana, kuma tana fatan yin kokari tare da ita wajen sa kaimi ga dangantakar abokantaka irinta gargajiya tsakaninsu zuwa wani sabon mataki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China