Bugu da kari,gwamnatin ta yi fatali da zaben tare da yi Allah wadai da fadan da ya wakana a majalisar
Taro na musamman da kwamitin tsaro na kasar ya gudanar, tare da halartar shugaban kasar Somalia,da shugaban majalisar da aka soke ,da firaministan kasar, ya amince cewa, tattaunawar da 'yan majalisar kasar suka gudanar haramtacciya ce wadda ba ta da wani tasiri.
A dai taron da aka gudanar a ranar Labara ne fada ya barke a majalisar dokokin kasar,inda aka yi kaca-kaca da ginin majalisar kasar da kuma lalata wasu abubuwa ,abun da gwamnati ta yi Allah wadai a kai.
Gwamnati ta dauki matakan hana sake abkuwar irin wannan lamari tare da matakan gaggauta kammala sabon kudin tsarin mulki na kasa,da gudanar da zaben 'yan majalisar kasar kamar yadda taron tattaunawa na MDD na baya-baya da ya gudana a Mogadishu ya amince.
Kwamitin tsaro na kasar na yankin kohon Afirka ya umarci dukkan mambobin majalisar da su darajanta tsarin tarraya na rikon kwarya da ya kasance ginshikin dokokin kasar. (Abdou Halilou)