A cikin wata sanarwar da kwamitin ta raba ma 'yan jaridu lahadin nan,tace wannan dama ya kuma taimaka wajen karfafa kokarin da ake yi wajen inganta bude wata hanya na aiwatar da siyasa kamar yadda masu ruwa da tsaki suka tsara a birnin na Mogadishu a farkon watan satumban wannan shekara a matsayin shawaran da ya biyo bayan yarjejeniyar Kamfala a watan Juni da ya gabata.
Kwamitin a taronsa na 298 da aka yi ranar 17 ga wannan watan ya samu bayani game da halin da ake ciki a Somalia daga wajen kwamishinan zaman lafiya da sha'anin tsaro,wakilin gwamnatin rikon kwarya na kasar Somalia da kuma Kasar Habasha,har ma da Shugaban gamayar gwamnatoci ta fannin cigaba IGAD da kuma tarayyar kasashen larabawa da MDD.
Kwamitin ta yaba ma gwamantin rikon kwarya na Somaliya da kuma rundunar Kungiyar Tarayyar Kasashen Africa dangane da juriya da sadaukar da kai da suka yi sannan kuma ta sake mika babban yabo ga wadanda suka rasa rayukan su ko suka raunana a wajen wannan kokari na tabbatar da an samu biyan bukata.
Sanarwar tace kwamitin na kara jaddada yabawarta ga gwamnatocin kasashen Burundi da Uganda domin taimaka ma dawo da zaman lafiya da suka yi a Somalia. (Fatimah)