in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a warware batun Syria ta hanyar siyasa
2013-09-12 20:26:17 cri
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka da Rasha za su tattauna kan shirin sa-ido kan makamai masu guba na kasar Syria a ranar 12 ga wata a birnin Geneva. Daga baya, kwamitin sulhu na MDD zai yi shawarwari game da shirin. Kakakin fadar shugaban kasar Amurka ya bayyana a ranar 11 ga wata cewa, kasarsa ba ta tsara jadawali game da wannan shiri ba.

Game da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga bangarori daban daban da su yi shawarwari don cimma daidaito kan yadda za a aiwatar da shirin da abin ya shafa. A ganin gwamnatin kasar Sin kan batun kasar Syria, kamata ya yi a bi ka'idojin kasa da kasa na hana yin amfani da makamai masu guba, kana a warware batun ta hanyar siyasa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China