in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan watsa labaran Najeriya ya bukaci da a inganta tsaro a kan iyakokin Najeriya da Kamaru
2013-09-08 19:47:29 cri

Ministan watsa labarai na tarayyar Najeriya Labaran Maku ya yi Allah wadai da matsalar rashin tsaro dake addabar bakin iyakokin kasashen Najeriya da Kamaru, inda ya bukaci da a karfafa harkar tsaro a wadannan wurare.

Mista Maku ya fadi haka ne a yayin wani taron manema labarai da aka yi a ranar Asabar a birnin Abuja, inda ya jaddada cewa, akwai bukatar a sa ido sosai kan shigowar makamai cikin Najeriya ta bakin iyaka.

Maku ya ce, kwalliya ta riga ta biya kudin sabulu wajen kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno, Yobe da Adamawa dake arewa maso gabashin Najeriya, kuma idan aka tsaurara matakan tsaro a kan iyakar Najeriya da Kamaru, to za'a samu karin ci gaba.

"Ana fuskantar wasu matsaloli a kan iyakokin Najeriya da Kamaru, amma idan muka karfafa yanayin tsaro a kan iyakokin, ko shakka babu za'a iyar hana shigowar makamai cikin Najeriya," cewar kalaman mista Maku.

Har wa yau kuma, Maku ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su maida hankali da taimakawa hukumomin kasa domin tabbatar da tsaro. Ya ce, "shekarun baya Najeriya ba ta fama da matsalar tsaro, amma yanzu wannan matsala tana kamari kan iyakokinmu da sauran kasashe, shi ya sa dole ne kowa da kowa ya maida hankali a kanta ta yadda za'a tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya da ma Afrika baki daya." (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China