in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ba zata bada hadin kai ga manzon Amurka ba
2013-09-15 16:13:33 cri
Kasar Sudan ba zata bada hadin kai ba ga manzon Amurka kan maganar kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, mista Donal Booth, har sai in ya nuna goyon baya kan yarjejeniyoyin da Khartoum da Juba suka rattabawa hannu in ji ministan harkokin wajen kasar Sudan Ali Karti a ranar Asabar a yayin wani taron manema labarai. Shugaban diplomasiyyar kasar Sudan ya nuna cewa kasar Amurka na amfani da batun yankin Abyei domin lalata dangantakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

Wakilin Amurka da ya isa ranar Jumma'a a birnin Khartoum, ya samu ganawa da shugaban kwamitin hadin gwiwa na kasar Sudan kan sanya ido game da batun yankin Abyei (ALOC), mista Al-Khair Al-Fahim.

Bayan ganawarsa tare da Al-Fahim,Mista Booth ya furta cewa yana fatan fahimtar matsayin al'ummar Misseriya da kuma sauraren ra'ayinsu domin cimma mafita guda mai karko kan matsayin yankin Abyei.

Kasar Sudan ta Kudu ta bayyana cewa sun amince da ranar da tarayyar Afrika ta tsaida domin shirya zaben raba gardama kan matsayin Abyei a farkon watan Oktoba, a yayin da kasar Sudan take nuna adawa tare da yin kashedi kan duk wani yunkurin daukar matakan bisa radin kai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China