in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka: An kammala zagayen farko na gasar neman shiga cin kofin kwallon kafa na duniya
2013-09-13 16:18:44 cri

A wasannin zagayen farko ta yankin nahiyar Afirka, da ake yi domin neman shiga gasar cin kofin duniya a wannan karo, kungiyar kasar Nijeriya, Malawi, Namibia da kuma Kenya sune a rukunin F. Bayan gasanni 5 a tsakaninsu, kulaf din Nijeriya ya samu maki 9, ya kuma cimma nasarar lashe wasanni biyu, da kuma kunnen doki sau uku. Yin kunnen doki a wasan ta na karshe kadai zai bata damar shiga zagaye na gaba.

Bayan da kungiyar Nijeriya ta samu nasara karawarta da kasar Malawi, ta samu maki 12, tare da kasancewa ta farko a rukuninta na biyu.

Kana a wannan rana, an yi gasar karshe ta rukunin C a tsakanin kungiyar kasar Cote d'Ivoire da ta Morocco. Da yake kulaf din kasar Cote d'Ivoire ya riga ya tabbatar da kasancersa na farko a rukunin C, wannan gasa ba za ta canja sakamako ba. A karshe dai kungiyoyin biyu sun yi kunnen doki da ci 1 da 1 a gasar. Don haka kungiyar kasar Cote d'Ivoire ta samu maki 14, tare da kasancewa ta farko a rukunin, sai kuma Morocco dake biye a matsayi na biyu da maki 9.

Kuma a rukunin D, kulaf din kasar Ghana ya lashe Zambia a gasar rukunin ta karshe da ci biyu da daya, don haka Ghana ta zama a matsayin farko a rukunin D, za kuma ta kara da ragowar kasashe a zagayen gasar na biyu.

Bayan wannan samun wannan sakamako, mai horo na kungiyar kasar Ghana ya bayyana cewa, wannan gasa ta baiwa kulaf din sa wuya, kasancewar Kulaf din kasar Zambia na da karfi sosai, amma dukkan 'yan wasan kungiyarsa sun yi imani da cewa, za su cimma nasara a karshe. Wanda daga karshe dai hakan ne ya faru. Kana ya kara da cewa, kungiyarsa za ta ci gaba da yin kokari don cimma nasara a gasar zagaye na biyu, da kuma gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.

A tarihi, kungiyar kasar Ghana ta taba shiga gasar cin kofin duniya a shekarar 2006 da kuma 2010.

Bisa jadawalin gasar, kungiyoyi 10 da suka zama a matsayin na farko a rukuninsu za su kara a zagaye na biyu a watan Nuwanbar bana, domin fitar da kungiyoyi 5 da zasu shiga gasar cin kofin duniya da aka shirya gudanarwa a kasar Brazil a shekara mai zuwa. (Zainab)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China