Mr. Wen Jiabao, firaministan kasar Sin ya halarci bikin, kuma ya yi jawabi, inda ya jaddada cewa, har yanzu kasar Sin tana da muhimmiyar dama irin ta tarihi wajen neman ci gaba, idan an ci gaba da bunkasa masana'antu, mayar da yankunan karkara garuruwa, zamanintar da aikin gona, za a fitar da sabon karfin neman ci gaba, wanda tabbas ne tattalin arzikin kasar Sin zai ci gaba da samun bunkasuwa ba tare da wata tangarda ba.
Wen Jiabao ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri cikin shekaru 30 da suka gabata, musamman a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi amfani da muhimmiyar dama irin ta tarihi wajen samun bunkasuwa, har ma tattalin arziki da zaman al'ummarta sun samu sabon ci gaba fiye da kima.
A yayin bikin, Mr. Wen ya takaita sakamakon da kasar Sin ta samu cikin shekaru 10 da suka gabata ta fuskokin tattalin arziki da zaman al'umma daga bangarori biyar, wato na farko dai, kasar Sin ta tsaya kan matsayinta na kara da kuma sa ido kan yadda aka samu ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma daga dukkan fannoni. Sannan ta yi kokarin daidaita da kuma kyautata tsarin tattalin arziki domin kokarin kyautata ingancin tattalin arziki da samun karin moriya. Haka kuma in ji shi, Sin ta yi kokarin bunkasa zaman al'umma yayin da take bunkasa tattalin arziki, ta yadda za a iya tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama'a da ba da tabbaci ga zaman al'umma cikin adalci. Bugu da kari, kasar ta yi kokarin yin tsimin makamashi da kare muhalli, ta yadda za a iya samun ci gaba ba tare da wata tangarda ba. Daga karshe dai, ta yi kokarin karfafa yin gyare-gyare da kara bude kofarta ga kasashen duniya, ta yadda za a iya samun sabon karfi na kara samun ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma. (Sanusi Chen)