in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara gudanar da dandalin Davos don tattauna rikicin tattalin arzikin Turai da tasirinsa a duniya
2012-09-11 17:15:31 cri
An kaddamar da taron dandalin Davos na lokacin zafi karo na 6 a birnin Tianjing na kasar Sin a ranar 11 ga wata, bisa babban jigon 'kafa tattalin arziki na nan gaba', kana rikicin tattalin arzikin Turai da tasirinsa' ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa a kai.

Jeffrey Joerres, shugaban kamfanin Manpower Group shi ne ke jagorantar taron, kana manyan bakin dake halartar taron sun hada da firaministan kasar Denmark, Helle Thorning-Schmidt, da firaministan kasar Latvia, Valdis Dombrovskis, da mataimakin babban darektan asusun ba da lamuni na IMF Zhu Min, da darektan cibiyar binciken tsarin tattalin arzikin duniya na bai daya ta jami'ar Yele ta kasar Amurka. An ce wadannan baki dukkansu sun sa ran alheri kan makomar nahiyar Turai.

Firaministan kasar Demmark Helle Thorning-Schmidt ya bayyana cewa, gwamnatocin kasashen Turai sun riga sun yi kokari sosai, sai dai a nan gaba ana bukatar daukar karin matakai, haka kuma a wasu kasashe ana bukatar yin kwaskwarima ga tsarin siyasa.

A nasa bangare, mataimakin babban darektan asusun ba da lamuni na IMF Zhu Min ya ce tattalin arzikin duniya na fuskantar barazana a fannoni 4, wadanda suka hada da matsalar yawan cin bashi a kasashen Turai, gibin kudi na kasar Amurka, mawuyacin halin da wasu kasashe masu tattalin arziki ke fuskanta, da hauhawar farashin abinci. (Bello)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China