Hakan zai taimaka wajen habakar tattalin arzikin nahiyar a cikin tsawon lokaci, in ji kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu, mista Mac Maharaj a kwanan nan.
Shugaba Zuma zai yi amfani da wannan dama a taron Davos domin yayata shirin cigaban kasa na Afrika ta Kudu (PDN) da ya kasance wani hangen babbar kasa da Afrika ta Kudu take kokarin zama nan da shekarar 2030 in ji mista Maharaj. Fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta yi wannan sanarwa kafin tashin shugaba Zuma zuwa Davos na Switzerland
A yayin taron, mista Zuma zai gayyaci kamfanonin kasa da kasa ga zuba jari a cikin ayyukan gine gine na biliyoyin kudin Rands da zai taimaka ga kawo sauyin tattalin arziki da na jama'a a kasar bayan kammala wannan taro. Shugaba Zuma na kare yankin bunkasar gine gine tsakanin Arewa da Kudu na AU dake tashi daga Durban zuwa Dar-es-Salaam, da kuma fatan yayata shi a taron Davos, a cewar kakakin fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu. (Maman Ada)