Manzon musamman na shugaban Sin Xi Jinping zai halarci bikin rantsar da aikin sabon shugaban kasar Mali
2013-09-11 20:10:29
cri
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya sanar a gun taron manema labaru a yau Laraba 11 ga wata cewa, a matsayinsa na manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin kuma shugaban hukumar kula da harkokin kabilu ta kasar Wang Zhengwei zai halarci bikin rantsar da aikin sabon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da za a yi a ranar 19 ga wata bisa gayyatar da aka yi masa. (Zainab)