in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a gudanar da bikin FIMA karo na 9 a watan Nuwamba a Yamai na Nijar
2013-06-19 10:58:26 cri

Bikin nune-nunen tufafin kasa da kasa da na Afrika (FIMA) karo na 9 zai gudana daga ranar 20 zuwa 25 ga watan Nuwamba mai zuwa a birnin Yamai na kasar Nijar, a cewar wata majiya mai tushe a birnin. Bikin FIMA wani babban dandalin kasa da kasa ne na manyan shahararrun madinka, masu zanen tufafi, masu fasaha da kwararru a fannin model, kuma wani dandali na cudanya da sada zumunci na manyan mutane da kwararru a fannin dinke-dinken zamani na nahiyar Afrika.

Taken wannan biki na watan Nuwamban shekarar 2013 shi ne 'taimakon kirkire kirkire wajen shimfida zaman lafiya.'

A cewar ministan harkokin wajen kasar Nijar, Mohamed Bazoum, wannan biki ya zama abin alfahari wajen maido da martabar dinke dinken zamani na Afrika, da ba shi babban matsayi na bunkasa al'adun kasa da kasa, fiye da manufarsa ta bangaren al'ada. Haka kuma yana da kyau mu bayyana taimakon da wannan biki yake kawo wa wajen shimfida zaman lafiya, gafartawa juna da hada al'ummomi dake da bambancin al'adu wuri guda. Dalilin haka ne gwamnatin kasar Nijar ta dauki niyyar tallafawa wannan biki, wanda ya kasance abin farin ciki ga kasar Nijar da ma Afrika baki daya.

Alfanun da za'a samu na da yawa ta fuskar yawon bude ido, kayayyakin hannu, al'adu ga kasar Nijar.

A nasa bangare, shugaban FIMA, Seidnay Sidi Ahmed da aka fi sani da Alphadi ya bayyana cewa, bikin wannan karo zai fi mai da hankali kan zaman lafiya tare da taimakon hukumomin kasar Nijar, domin al'adu na taimakawa wajen samar da zaman lafiya, domin ta zaman lafiya ne kadai za'a samu cigaba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China