A ranar Jumma'a 6 ga wata a birnin St. Petersburg na kasar Rasha, kasar Spain da shugabanni ko wakilai na kasashe membobin kungiyar G20 guda 9 wato Australia, Canada, Faransa, Italiya, Japan, Koriya ta Kudu, Saudiya, Turkiya, da Birtaniya sun rattaba hannu kan wata hadaddiyar sanarwa tare da kasar Amurka, wadda ke kunshe da Allah wadai da gwamnatin Syria, bisa amanar da suka yi cewa, mahukuntanta sun yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula. Kasashen dai na tabbatar da goyon baya da sukewa kokarin Amurka, da hadin gwiwar wasu kasashen duniya, na dakatar da amfani da makamai masu guba.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana daukar wani alkawari na taimakawa daukar matakin soji kan kasar ta Syria ba.(Fatima)