Zababben shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita da aka fi sani da IBK ya yi rantsuwar kama aiki a ranar Laraba a gaban mambobin kotun kolin kasar a yayin wani babban bikin rantsar da shi da aka shirya a dakin tarurukan kasa da kasa dake birnin Bamako (CICB). A yayin wannan biki, shugaban kotun kolin kasar Mali, Nouhoum Tapily ya bayyana cewa, kotun koli ta amince da rantsuwar sabon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita. Sabon shugaban kasar Mali na rantsuwa gaban Allah da al'ummar kasar Mali. 'Zan bautawa kasa ta hanyar kiyaye da kare tsarin mulkin kasa, da yin aiki yadda ya kamata domin moriyar 'yan kasar Mali, da kare tsarin demokaradiyya, tabbatar da hadin kan kasa, 'yancin kasa da cikakken yankin kasa.' in ji sabon shugaban kasar Mali a gaban shugabannin kasashen waje da manyan jami'ai da suka halarci wannan biki. 'Na dauki niyyar cigaba da awaitar da duk wasu ayyukan da za su taimaka ga cimma hadin kan 'yan kasar Mali baki daya.' in ji Ibrahim Boubacar keita a cikin jawabinsa. (Maman Ada)