Shugaban wucin gadin kasar Mali, Dioncounda Traore ya jagoranci wani zaman taron mininstoci na musammun a ranar Litinin a birnin Bamako. A yayin wannan haduwa, mista Traore ya nuna yabo cikin kalamai masu sosa rai ga dukkan mambobin gwamnati tare da ba su takardar yabo, haka ma wasu manyan jami'ai fararen hula da sojoji sun samu takardun karamawa daga hannun mista Dioncounda Traore.
Zaman taron ministocin ya gudana kwanaki biyu kafin sabon shugaban kasar da aka zaba Ibrahim Boubacar Keita ya yi rantsuwar kama aiki.
A cikin jawabinsa, mista Traore ya bayyana cewa, wannan wani nufi ne na kiran mambobin gwamnati da su bautawa kasa, tare da nuna cewa, kowa ya yi imani da nauyin aikin dake bisa wuyanmu da kuma yanayin da kasarmu take ciki.
Haka kuma mista Traore ya jinjinawa gamayyar kasa da kasa game da goyon baya da taimakon da ta baiwa kasar Mali. (Maman Ada)