Bayan da kotun kolin kasar Mali ta ba da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar zagaye na biyu wanda ya tabbatar da nasarar Ibrahim Boubacar Keita (IBK), Mamadou Diawara, mai magana da yawun 'dan takara Soumaila Cisse, ya jaddada a ranar Talata cewa, da farko ya kamata gwamnati ta fara yin shawarwari tare da jam'iyyun siyasa domin tsai da lokacin zabubukan 'yan majalisar dokoki.
Dan takarar jam'iyyar RPM, malam Ibrahim Boubacar Keita wato IBK da Soumaila Cisse na jam'iyyar URD kowanensu ya samu kashi 77,62 cikin 100 da kashi 22,38 cikin 100 bisa yawan kuri'un da suka samu bayan zaben shugaban kasa zagaye na biyu, da ya gudana a ranar 11 ga watan Agustan da ya gabata, tare da samun halartar kashi 45,73 cikin 100 na mutanen kasar. Kuma shugaban kotun kolin kasar ya sanar da wannan sakamakon na din din din. Da yake magana kan zabubukan 'yan majalisa na gaba, mai magana da yawun mista Cisse ya yi tunanin cewa, ya kamata a ba da lokaci, ta yadda za'a samu damar tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa da gwamnati domin daukar matakan da suka dace.
'Yana da kyau a tabbatar da tsarin tattaunawa tsakanin jam'iyyun siyasa da gwamnatin da farko, ta yadda za'a tsai da lokacin da ko wane bangare zai amincewa da shi.' in ji mista Diawara. (Maman Ada)