A yayin wata hirarsa ta farko tare da sabon shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya jaddada a ranar Laraba niyyar MDD na cigaba da tallafawa tsarin siyasa na wannan kasa.
Mista Ban ya nuna yabo kan yadda aka gudanar da zabubukan siyasa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan kasa da kuma gabatar da taimakon MDD wajen aiwatar da yarjejeniyar ranar 19 ga watan Juni tsakanin gwamnatin kasar Mali da gungun kungiyoyin da suka dauki makamai a arewacin kasar.
Haka zalika, babban jami'in MDD ya tabbatar da niyyar kungiyarsa ga taimakawa gwamnatin Mali kan kokarin da take na warware tushen wannan rikici, musamman ma ta hanyar yin shawarwari da hadin kan 'yan kasa, in ji kakakin mista Ban a cikin wata sanarwa.
Zaben shugaban kasa ya kasance muhimmin mataki na kokarin sake gina kasar Mali. Tun farkon shekarar 2012, kasar ta yi fama da juyin mulkin soja, sake barkwar yaki tsakanin sojojin gwamnati da 'yan tawayen Abzinawa, da kuma fadawar arewacin kasar a hannun 'yan kishin islama.
Manzon musamman na mista Ban game da yankin Sahel, Romano Prodi shi ma ya taya shugaba Keita da ya ci zabe, da kuma yabawa matakin Soumaila Cisse da ya amince da sakamakon zabe domin taimakawa zaman lafiya da demokaradiyya a kasar Mali da ma shiyyar baki daya. (Maman Ada)