in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata matakin soja kan Syria ya samu amincewar kwamitin tsaron MDD, in ji Brahimi
2013-08-29 14:36:34 cri

Duk wani matakin soja da za'a dauka kan kasar Syria ya kamata ya samu amincewar kwamitin tsaro na MDD, a wani kashedin manzon musamman na tarayyar kasashen Larabawa da MDD, mista Lakhdar Brahimi a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Laraba a Geneva. Dokar kasa da kasa ta bayyana cewa, duk wani matakin soja da za'a dauka kan wata kasa ya dace ya samu amincewar kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, in ji wannan jami'i.

'Har yanzu na yi imanin cewa, babu wata hanyar warware matsalar Syria ta amfani da matakin soja, amma akwai hanya guda ta warware wannan matsala ita ce, hanyar siyasa.' in ji mista Brahimi. A cewarsa, ya zama wajibi a gane muhimmancin warware bisa turbar diplomasiyya da nuna goyon baya kan matakin siyasa maimakon matakin soja.

A san cewa, rikicin kasar Syria matsala ce mafi muni a halin yanzu ga gamayyar kasa da kasa, in ji mista Brahimi, kuma ya kara da cewa, ya tuntubi Amurka da Rasha, da suka nuna fatansu na ganin an shirya dandalin Geneva na biyu.

Masu adawa da gwamnatin Syria sun bayyana cewa, mutane 1300 suka mutu bayan harin sojojin gwamnatin Syria suka kai da makamai masu guba a wasu sansanonin 'yan tawaye dake karkarar birnin Damascus a ranar Laraban da ta gabata. Sai dai gwamnatin Syria ta karyata wannan zargi da babbar murya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China