Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya ja kunnen dukkan bangarorin da abin ya shafa game da batun Syria, da kada su yi riga malam masallaci wajen daukar matakan soja kafin samun sakamakon masu gudanar da bincike na MDD, yayin da gwamnatin Amurka ke kamfel din neman samun goyon bayan majalisar dokokin kasar don kai hari kan Syria.
Mr. Ban ya bayyana hakan ne ranar Talata, yayin taron manema labarai a hedkwatar majalisar kafin ya tashi zuwa St. Petersburg na kasar Rasha don halartar taron kolin kungiyar kasashen G20 da aka shirya gudanarwa daga ranar Alhamis zuwa Jumma'a.
Sakataren janar MDD ya ce, a ranar Laraba ne ake sa ran dukkan samfurin sinadarai da aka tattara a wurin da ake zargin an kai hari da makamai masu guba a ranar 21 ga watan Agusta, inda daruruwan fararen hula suka halaka, za su isa dakunan gwaje-gwajen da aka tanada.
Idan ba a manta ba, a ranar Asabar ne sifetocin MDD dake bincke a kasar Syria, suka kammala aikinsu, inda shugaba Barack Obama na Amurka ya zargi gwamnatin Syria da amfani da makamai masu guba kan fararen hula a wajen Damascus, kana ya bukaci iznin majalisar dokokin kasar don daukar matakan soja kan gwamnatin Syria.
Ban Ki-moon dai ya yi kiran da kada a yi hanzarin kai hari kan Syria, inda ya ce, kwararru na aiki ba dare ba rana don ganin sun kammala aikinsu cikin hanzari. Bugu da kari, ya jaddada muhimmancin kai zuciya nesa domin kada a kawo kafar ungula ga binciken da ake yi.
Ya ce, ya yi wa kwamitin sulhu mai mambobi 15 bayani game da matsayin binciken, kana babbar wakiliyar MDD mai kula da kwance damarar makamai Angela Kane, za ta yi wa sauran kasashe mambobi bayani a wani lokaci a yau.
Mr. Ban ya bayyana karara cewa, ba za a amince da amfani da makamai masu guba ba, kana ya yi kira ga kasashe mambobin kwamitin sulhu da su hada kai wajen daukar matakan da suka dace, idan har zargin amfani da makamai masu guba din da ake yi ya tabbata gaskiya. (Ibrahim)