in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Afrika ta Kudu ya jaddada matsayin MDD kan warware rikicin Syria
2013-09-03 14:26:53 cri

MDD kadai ce take da ikon daukar matakin kai harin soja kan duk wata kasa, idan kuma har duk wasu hanyoyin neman sulhu cikin ruwan sanyi sun kare, in ji shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma. 'Muna fatan ba'a take dokar kasa da kasa ba ko yin amfani da kwamitin tsaro na MDD ba bisa ka'ida ba domin cimma burin wasu kasashe.' in ji mista Zuma bisa la'akari da barazanar Amurka take na kaiwa Syria harin soja bisa zargin cewa, gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kan fararen hula a karkarar birinin Damuscus a cikin watan da ya gabata. Bisa tushen zaman lafiya ne kawai duniya za ta iyar cigaba da zaman karko, musamman ma a kasashe masu tasowa dake fama da kalubalolin da suka shafi tattalin arziki, tsaro da zaman lafiya kuma muna fatan cewa, za'a girmama MDD a matsayin babbar hukumar duniya da take da hurumin daukar matakin soja kan duk wata kasa idan har tattaunawa da shawarwari suka kasa, in ji mista Zuma tare da jaddada fatan zaman lafiya a nahiyar Afrika, musammun ma a kasashen Masar da gabashin DRC-Congo. Haka zalika shugaban kasar Afrika ta Kudu ya bayyana cewa, ya kamata zaman lafiya da demokaradiyya su kasance jagora a ko wane bangare na Afrika da na duniya baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China